in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wassu 'yan bindiga sun hallaka mutane fiye da 45 a Nijeriya
2014-01-28 10:00:26 cri
Rundunar 'yan sanda a Nijeriya a litinin din nan suka tabbatar da cewa mutane da dama sun rasa rayukan su a wani hari da wassu 'yan bindiga suka kai a karamar hukumar Konduga dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar,wanda nan ne cibiyar kungiyar nan ta boko haram.

Kwamishinan 'yan sanda a jihar Lawan Tanko ya sheda ma Xinhua a Maiduguri babban birnin jihar cewa an gano gawawwakin mutane 45 duk da cewar yawan wadanda suka halaka zai iya fin hakan saboda har yanzu ana cigaba da kirgar wadanda suka rasa rayukan su, kuma akwai akalla mutane 26 da aka kai asibiti.

Wata majiya ta ce maharan sun tsere bayan harin cikin dajin Sambisa wanda a kwanakin nan ya zama maboyar 'yan kungiyar ta boko haram.

Ya zuwa lokacin da labarin ya iso babu wani mutum ko wata kungiya da ta dauki alhakin wannan harin, sai dai an san jihar ce cibiyar wannan kungiya na masu tsattsauran ra'ayin addini,wanda ke barazana ga zaman lafiya da tsaro a kasar dake yammacin Afrika. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China