Shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan ya sanar a ranar 16 ga wata cewa, shugaban jam'iyyar PDP malam Tukur ya yi murabus a wannan rana. Shugaba Jonathan ya ce, Tukur bai yi wani laifi ba, don haka a nan gaba za a kara ba shi wani babban aiki.
Ya yi bayanin cewa, a ranar Litinin mai zuwa wato 20 ga wata, jam'iyyar za ta sake shirya cikakken taron kwamitin zartaswa, inda za a sanar da sunan sabon shugaba.
Bisa labarin da muka samu, an ce, malam Tukur ya gabatar da takardar murabus dinsa ne a gun cikakken taron kwamitin zartaswa na jam'iyyar, wanda aka shirya a wannan rana a Abuja, babban birnin kasar Nijeriya.
Tun daga bara, aka fara samun sabani a cikin jam'iyyar ta PDP wadda ke rike da karagar mulkin kasar, shugabanni da yawa na jam'iyyar suna ta matsin lamba ga malam Bamanga Tukur, tare da zargin cewa, bai dauki matakai da su kamata ba yayin daidaita rikicin jam'iyyar, don haka ya kamata ya sauka daga mukaminsa. Sai dai shi kuma Bamanga Tukur ya dage akan cewa, zai yi iyakacin kokarinsa don tafiyar da harkokin jam'iyyar yadda ya kamata, kuma ya ce, ba zai sauka daga mukaminsa ba.
To sai dai kuma a wannan ranar da Bamanga Tukur ya sauka daga mukaminsa, fadar shugaban kasar Nijeriya ta sanar da sauyin manyan hafsoshin kasar guda hudu tare da na da wadanda za su maye gurbinsu.
Sanarwar sai dai ba ta bayyana dalilin wannan sauyi ba, amma wasu jama'a na cewa, wannan matakin da aka dauka yana da nasaba da niyyar kyautata halin tsaro a kasar, da kuma kara yaki da kungiyar nan ta Boko Haram.(Danladi)