in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Koyar da fasahar tsayawa dogara da kai, fasaha ce mafi nagarta a fannin yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka
2014-01-31 20:34:36 cri
Kwanan baya, Xie Xiaoyan, wakilin kasar Sin da ke kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU ya ce, yin zaman daidai wa daida da neman samun moriyar juna da kuma koyar da fasahar tsayawa da kafafu, za su iya taimaka wa kasar Sin baje kolinta a nahiyar Afirka, kuma su ne fasahohi mafiya nagarta ta fuskar yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka.

Yanzu ana gudanar da taron shugabannin kungiyar AU a birnin Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha. Mista Xie ya nuna cewa, a lokacin ziyarar shugaba Xi Jinping na kasar Sin zuwa Afirka a shekarar 2013, ya ce, Sin da Afirka suna hada kansu kamar 'yan uwa ba tare da rufe-rufe ba a hakikanin fannoni. Ya kuma yi kira da Sin da Afirka da su kara samun bunkasuwar moriyar juna. Mista Xie ya kara da cewa, kada a mai da hankali kan samun moriya kawai yayin da ake hada kai da kasashen Afirka. Ba za a iya samun hadin gwiwa mai dorewa tare da kasashen Afirka ba, idan aka zura ido kan samun riba kawai.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China