An yi taron dandalin tattaunawa tsakanin shugabannin kamfanonin Sin da Afirka da kuma taron tattaunawa kan hadin gwiwar ayyukan noma tsakanin Sin da Afirka, bisa babban taken taro na wannan karo, watau "hadin gwiwa da cimma moriyar juna".
A yayin taron, jami'an ma'aikatar harkokin ayyukan noma ta kasar Sin, masanan ayyukan noma na Sin, jami'an kasashen Afirka da kuma jakadun Afirka dake kasar Sin sun cimma ra'ayi daya cewa, ta hanyar yin hadin gwiwa kan ayyukan noma, Sin za ta iya koyar da kasashen Afirka fasahohin ayyukan noma na zamani ta yadda za ta ba da taimako gare su wajen warware matsalar karancin abinci. (Maryam)