An yi tattaunawa kan kara yin hadin gwiwa da samun ci gaba a gidajen kiyaye kayayyakin tarihi na Sin da kasashen Afirka
Ma'aikatar harkokin al'adun kasar Sin ta gudanar da dandalin tattaunawa a tsakanin shugabannin gidajen kiyaye kayayyakin tarihi na kasar Sin da kasashen Afirka a yau Litinin 18 ga wata a nan birnin Beijing. A gun taron mai taken "samun ci gaba da yin hadin gwiwa a tsakanin gidajen kiyaye kayayyakin tarihi na Sin da kasashen Afirka", wakilai dake halartar taron sun yi tattaunawa a fannonin manufofin raya gidajen kiyaye kayayyakin tarihi na Sin da kasashen Afirka, yanayi da makomar gidajen, hadin gwiwa da dai sauransu.
Mataimakin shugaban sashen kula da harkokin kasashen waje na ma'aikatar al'adun kasar Sin Zhao Haisheng ya yi jawabi a gun taron, inda ya ce, dandalin tattaunawar yana da babbar ma'ana wajen kara yin mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a fannin al'adu. (Zainab)