Kwanan baya, a yayin da Abe Shinzo, firaministan kasar Japan ke ziyara a kasashen Afirka, Japan ta ce, nufin kasar Sin na taimakawa Afirka shi ne yunkurin sayar da kayayyakinta a kasuwannin Afirka da kwace albarkatun Afirka. Japan ta kuma yi shelar cewa, Japan ta sha bamban da Sin, saboda ta kara samar wa 'yan Afirka guraben aikin yi.
Dangane da haka, a yayin taron manema labaru da a kan shirya a nan Beijing, Hong Lei ya ce, abun da Japan ta fada, abin dariya ne. Kasar Sin ta dade tana bai wa Afirka taimako ba tare da nuna son kai ba a fannonin kara raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasashen Afirka da kyautata zaman rayuwar 'yan Afirka bisa ka'idar taimakawa juna a karkashin tsarin yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa.
Hong Lei ya kara da cewa, kasar Sin na fatan Japan za ta cika alkawarin da ta yi na bai wa Afirka yawan taimako kamar yadda firaministan Japan ya bayyana a lokacin ziyararsa a Afirka a wannan karo. Kasar Sin za ta zura ido kan yadda Japan za ta cika alkawarinta. (Tasallah)