in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban kasar Sin ya yi shawarwari da takwaransa na Afirka ta Kudu
2013-10-28 21:00:46 cri
A ranar Litinin 28 ga wata, mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao ya jagoranci taron kwamitin kula da harkoki tsakanin Sin da Afirka ta Kudu karo na biyar tare da takwaransa na Afirka ta Kudu Kgalema Motlanthe a nan birnin Beijing inda suka yi shawarwari kan yadda za a zurfafa hakikanin hadin gwiwa tsakaninsu, tare da cimma matsaya daya.

Kafin taron, Mataimakan Shuagabannin kasashen biyu sun kira tarurrukan kananan kwamitoci kan diplomasiyya, tattalin arziki da cinikayya, kimiya da fasaha, ma'adinai, da kuma makamashi.

A yammacin wannan rana, har ila yau, Mr Li ya shirya bikin maraba ga takwaranasa mista Motlanthe, sannan daga baya su biyu suka halarci bikin sa hannu kan yarjejeniyoyi a fannonin yawon shakatawa, harkokin gwamnati da dai sauransu tsakanin kasashen biyu.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China