in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana son cimma burin farfadon kasa tare da Afirka
2014-01-07 11:05:42 cri

A ran 6 ga wata a yayin da ministocin harkokin wajen Sin Wang Yi da Habasha Tedros Adhanom Ghebreyesus suke zantawa tare da manema labaru bayan ganawarsu, Mista Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana son cimma burin farfadon kasa, da samun bunkasuwa mai albarka, da zaman lafiya tare da kasashen Afirka.

Wang ya ce, kasar Sin tana da kyakkyawar manufa a fannin diplomasiyya, wato ziyara ta farko da ministan harkokin wajenta ya kan yi a farkon ko wace shekara, tabbatas ne ya zo Afirka. Dalilin da ya sanya hakan shi ne kasar Sin tana son isa da sako ga duniya cewa, Sin tana son inganta hadin kai da kasashen Afirka, wannan dai ya zama wani babban tushe mai muhimmanci ga manufofin diplomasiyyar Sin. Ya kara da cewa, shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya bayyana a fili cewa, bangarorin Sin da Afirka har kullum su zama tare, a matsayin 'yan uwa da ba za a iya raba su ba. Ko ta wane halin yanayin duniya, Sin za ta tsaya kan matsayinta game da 'yan uwa na Afirka, kuma Sin za ta kasance 'yar uwa da abokiya da kasashen Afirka.

Wang ya karfafa cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kasashen Afirka wajen zaben hanyoyin da suka dace da hakikanin halin da suke ciki, da kara gaggauta dunkulewar Afirka wuri daya, da warware matsalolinsu da kansu, da nuna goyon baya ga Afirka wajen samun babban matsayi yadda ya kamata, ta yadda su ma za su bayar da taimakonsu a cikin harkokin duniya.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China