Tsohon shugaban kungiyar AU na wannan zagaye, firaministan kasar Habasha Hailemariam Dessalegn ya ba da wani jawabi a yayin bikin bude taron, inda ya nuna yabo ga sakamakon da nahiyar Afirka ta samu dangane da gudanar da shirin raya ayyukan noma na kasashen Afirka bisa dukkan fannoni cikin shekaru goma da suka gabata. A sa'i daya kuma, ya bayyana cewa, ya kamata kasashen Afirka su dukufa tare wajen shimfida zaman lafiya da na karko a kasar Sudan ta Kudu da kuma kasar Afirka ta Tsakiya, kada rikice-rikice na wasu kananan yankuna ya bata yanayin tsaron nahiyar Afirka gaba daya.
Shugabar hukumar zartaswar kungiyar AU Dlamini Zuma ta kuma ba da wani jawabi inda ta nuna fatanta ga nahiyar Afirka a shekarar 2063, da kuma aniyarta wajen cimma wannan burin. (Maryam)