Zaunannen taron kwamitin zartaswa na kungiyar AU karo na 24 da za'a shafe kwanaki 2 ana yinsa ya zama taron share fagen taron koli na kungiyar AU. Ko da yake, taken taron bana shi ne, aikin gona da samar da isasshen abinci, amma yanzu, yake-yaken da ake fuskanata a jamhuriya Afrika ta Tsakiya da Sudan ta Kudu, da rikicin jin kai sun sa kokarin kiyaye zaman lafiya da karko ya zama abu mai muhimmanci da mahalartar taron suka dora muhimmanci sosai a kai.
Mahalartar taron zasu tattauna batun tsaro da nahiyar Afrika ke fuskanta, da lalubo bakin zaren warware batun. A gun taron da aka bude a wannan rana, bangarorin daban daban sun tsaida kudurin mai da Madagascar kujerarta a kungiyar AU.
A gun bikin bude taron, shugabar kwamitin kungiyar AU Madam Nkosazana Dlamini-Zuma ta bayyana cewa, a cikin shekarar da ta gabata, kungiyar AU za ta hada gwiwa da kasashen duniya, inda suka samu babban ci gaba wajen warware batutuwan tsaro na Somaliya, Mali da Madagascar.
Ta yi bayanin cewa nahiyar Afrika na ci gaba da fuskantar kalubale tsaro mai tsanani, don haka inji ta,dole ne a samar da zamantakewar al'umma masu hakuri, da samun sulhuntawa, da girmama hakkin dan Adam.
A sa'i daya kuma, dole ne a bukaci shugabanni da su sauke nauyi bisa wuyansu. Sabo da haka, ta ba da shawara da kara girmama hakkin dan Adam da hakkin kotun sunhuntawa tsakanin kabilu daban daban a kasashen Afrika.(Bako)