Madam Zuma ta yi wannan kira ne yayin da take halartar taron koli karo na 33 na kungiyar raya kudancin Afirka, wato SADC a birnin Lilongwe, hedkwatar mulkin kasar Malawi.
Ta bayyana cewa, kungiyar AU na nuna kulawa sosai kan batun tashin hankali da zubar da jini da ke faruwa a kasar Masar. Kana ta yi kira ga bangarori daban daban na kasar da suyi hakuri, su kuma kaddamar da tattaunawa a tsakaninsu cikin hanzari domin samun sulhu.
Haka zakila, Madam Zuma ta ce, kungiyar AU ta riga ta tura wata kungiyar kwararru ta babban mataki zuwa Masar. Idan ba za a iya kwantar da kurar da ta tashi a kasar ba, to kungiyar AU za ta duba yiwuwar kiran taron musamman na kwamitin kula da zaman lafiya da tsaro domin tattaunawa kan batun sa hannu cikin halin da Masar ke ciki.
Tun daga 14 ga wata ne, sojoji da 'yan sanda na kasar Masar suka fara korar masu zanga-zanga masu goyon bayan Mahammad Morsy a wasu filaye biyu da ke birnin Alkahira, lamarin da ya haddasa abkuwar rikice-rikice a wurare da dama a duk fadin kasar, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar da mutane masu dimbin yawa.(Kande Gao)