A yayin ganawar tare da 'yan jarida a jajibirin babban taron kungiyar karo na 22 bisa taken "Noma da Tsaron abinci", shugabar AU, 'yar asalin kasar Afrika ta Kudu ta yi kira da a kara himmatuwa wajen bunkasa aikin noma a nahiyar Afrika.
Baya ga daidaita tasirin karuwar al'umma a fannin noma, bunkasa samar da albarkatun noma da kyautata ayyukan gine-gine da kayyayakin aiki a bangaren noma, madam Zuma ta yi kira da a kara azama wajen jawo hankalin matasa shiga aikin noma. Ya kamata mu bullo da wasu dabaru domin kyautata aikin noma ta yadda matasa za su ji sha'awar rungumarsu, in ji wannan babbar jami'a.
A wani labari na daban kuma, madam Zuma ta karyata jita jitar dake bayyana cewa tana shirin barin mukaminta domin maida hankali ga shirye shiryen shiga zabubuka masu zuwa a cikin kasarta inda ta ce sai ta kammala wa'adinta yadda ya kamata, idan har tana raye. (Maman Ada)