A gun bikin rufe taron, shugaban kungiyar AU a wannan karo, kana firaministan Habasha Hailemariam Dessalegn ya yi jawabi cewa, a wannan taro, kasashe mahalarta taron sun cimma matsaya daya, inda suka bukaci kotun hukunta manyan laifukan duniya da ta yi taka-tsamtsam da kuma sauraron muryar kasashen Afirka, kuma ta bi ka'idojin duniya, wato kada ta yanke hukunci ga shugabannin kasa dake kan mulki. Ya ce, a kokarin kiyaye kundin tsarin mulki, da tabbatar da zaman lafiya da ikon mulkin kasa, kungiyar AU tana ganin cewa, bai kamata wata kotun kasa da kasa ta gurfanar da shugabannin kasashe membobin kungiyar AU dake kan mulki a gaban kotu ko kuma ci gaba da yanke hukunci kansu ba.(Fatima)