Rahoton ya ce, alkaluman za su taimakawa gwamnatocin kasa da kasa wajen yanke shawara da daukar matakai, ta yadda za a ceci miliyoyin kananan yara da kuma kyautata zaman rayuwarsu.
Rahoton ya kara da cewa, tun bayan da aka kaddamar da yarjejeniyar kiyaye hakkokin kananan yara a shekarar 1989 zuwa yanzu, kasashen duniya sun samu babban ci gaba wajen kyautata halin da yara suke ciki, yayin da suke kokarin tabbatar da manufar bunkasuwa ta MDGs a shekarar 2015.
A sa'i daya kuma, rahoton ya nuna cewa, ya zuwa yanzu ana keta hakkokin kananan yara a wasu sassan duniya, haka kuma, alkaluman sun tono matsalar rashin adalci da kuma bambance-bambance iri daban daban da ake fuskanta a halin yanzu. (Tasallah)