in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Japan yana kan hanyar kai ziyara yankin Gabas ta Tsakiya da nahiyar Afirka
2014-01-09 11:03:07 cri

Rahotanni daga Japan na cewa, a ranar Alhamis ne firaministan kasar Shinzo Abe, zai tashi zuwa yankin Gabas ta Tsakiya da nahiyar Afirka, a wani kokari na bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki da shiyyoyin biyu, ta yadda kasar ta Japan za ta samu zarafin shigo da makamashi tare da bunkasa kayayyakin da take fitarwa zuwa ketare.

Ziyarar ta mako guda, za ta kai Abe zuwa Oman, babban birnin kasar Jordan, zangon farko a ziyarar da zai kai kasashen hudu da kuma kasashen Ivory Coast, Mozambique da Habasha a nahiyar Afirka.

Bugu da kari, ana sa ran Abe zai gana da sarkin Oman, Qaboos bin Sa'id, inda zai yi kira ga kasar da ke yankin Gulf, da ta samarwa kasar ta Japan mai da iskar gas.

Kafofin watsa labarai sun kuma bayyana cewa, ana sa ran yayin ziyarar tasa a kasashen uku na Afirka, Abe zai bayyana ci gaban kasar ta Japan na goyon bayan bunkasuwar nahiyar ta Afirka, musamman a fannonin kayayyakin more rayuwa, da kuma horas da ma'aikata. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China