Majalisar dinkin duniya, ta yi kira ga mahukuntan jamhuriyar demomiradiyar Congo (DRC) da su hanzarta daukar matakai, biyo bayan rahotannin da ake samu game da bacewa da halaka yara da matasa a Kinshasa, babban birnin kasar.
Asusun tallafawa yara na MDD (UNICEF) da tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD da ke jamhuriyar demokiradiyar Congo (MONUSCO) sun bayar da wata sanarwa a ranar Laraba da ke nuna cewa, akwai wasu bayanai da a halin yanzu ake kokarin tantancewa da ke tabbatar da cewa, a kalla mutane 20, ciki har da yara 12 ne aka bayar da rahoton mutuwarsu.
Sanarwar ta ce, wajibi ne hukumomin shari'a su gudanar da bincike, ta yadda za a gurfanar da wadanda suka aikata wannan laifi a gaban kuliya, kamar yadda dokokin da suka shafi hukunta masu aikata manyan laifuffuka na kasar Congo suka tanada.
Kungiyoyin biyu na cewa, rahotannin da ake samu game da asarar rayukan jama'a, na zuwa ne dai-dai lokacin da hukumomin kasar ta Congo suka fara kaddamar da wani shiri mai suna "Operation Likofi" daga ranar 15 ga watan Nuwamba zuwa 15 ga watan Fabarirun shekara mai zuwa da nufin kakkabe miyagun lafuffukan da kananan yara suke aikatawa a birane.
UNICEF da MONUSCO sun kuma yi kira ga hukumomin kasar ta Congo, da su hanzarta daukar matakai don kawo karshen wannan matsala, tabbatar da kare 'yancin bil-adama, tare da baiwa yara kulawa ta musamman kamar yadda dokokin kasar da na kasa da kasa suka shimfida.
MDD dai ta nanata kudurin na taimakawa gwamnatin Congo, a kokarin da take yi na warware matsalolin da suka shafi rayuwar yara da matasa. (Ibrahim)