Mataimakiyar faraminstan kasar Sin Liu Yandong ta isa birnin Addis Abeba na kasar Habasha a ranar Lahadi, ta fara wata ziyarar aiki ta kwanaki uku a nan.
Madam Liu za ta yi tattaunawa tare da shugaban kasar Habasha, faraministan kasar da kuma mataimakin faraminsta a yayin wannan rangadi nata a kasar Habasha, in ji darekta janar na ma'aikatar harkokin wajen kasar Habasha dake kula da harkokin shiyyar Asiya da Oceania, mista Genet Teshome.
Jami'in ya bayyana cewa, wannan ziyarar aiki ta tawagar kasar Sin ta kasance wani kashi na karfafa huldar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, musamman ma a fannonin da suka shafi kiwon lafiya, ilmi, kimiyya da fasaha, ya kuma jaddada cewa, bangarorin biyu za su sanya hannu kan wasu jerin yarjejeniyoyi guda takwas, ko wani kundin dake kunshe da batutuwan hadin gwiwa a fannonin ba da ilmi, bincike da musanyar al'adu tsakanin kasashen biyu. (Maman Ada)