in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Chadi ya fara wata ziyara a kasar Sudan
2013-12-24 09:32:10 cri

A ranar Litinin ne shugaban kasar Chadi Idriss Deby, ya isa Khartoum, babban birnin kasar Sudan, don fara wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu, inda ake sa ran zai tattauna da takwaransa na kasar Sudan Omar al-Bashir game da batutuwan da ke shafar kasashen biyu.

Ministan watsa labarai na kasar ta Sudan Yassir Yousif ne ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce, ziyarar ta Mr. Deby ta zo a dai-dai muhimmin lokacin da ya dace bisa ga la'akari da dangantakar siyasa da tsaro da ke tsakanin Khartoum da N'djamena.

Ya ce, ziyarar ci gaba kan tattaunawar da bangarorin biyu ke yi game da muhimman batutuwan da suka shafi tsaro a kan iyakokin kasashen biyu da kuma rikicin da ke faruwa a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da sauran kasashen da ke shiyyar.

Bayanai na nuna cewa, dangantaka tsakanin sassan biyu ta karfafa a baya, inda bangarorin biyu suka kara karfafa ta tare da sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro, kana suka lashi takwabin dakatar da marawa kungiyoyin 'yan tawaye dake kasashensu baya tare da tura dakarun hadin gwiwa zuwa kan iyakokinsu da nufin inganta tsaro. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China