in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ya yi kwarya-kwaryar gyaran fuska a majalisar zartaswar kasar
2013-12-09 10:06:53 cri

A ranar Lahadi ne shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir, ya bayar da wasu dokokin jamhuriya wadanda ke amincewa da shawarar da jam'iyya mai mulki ta kasar NCP ta bayar game da yi wa majalisar zartaswar kasar kwarya-kwaryar gyaran fuska.

Bisa ga tsarin dokokin, an nada janar Bakry Hassan Salih a matsayin mataimakin shugaban kasa na farko, Hassabo Mohamed Abdul-Rahman mataimakin shugaban kasa yayin da aka nada Ibrahim Ghandour a matsayin mataimaki ga shugaban jamhuriya.

Bugu da kari, a cewar dokokin, al-Bashir ya amince da nadin sunayen ministocin da jam'iyyar NCP ta gabatar, ko da yake da farko jam'iyyar NCP ta sanar da cewa, gyaran fuskar za ta shafi ministocin jam'iyyar ce kawai.

A ranar Litinin ne ake sa ran za a rantsar da sabbin ministocin da aka nada. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China