in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sudan da Eritrea sun lashi takwabin bunkasa dangantakar dake tsakaninsu
2013-11-26 09:53:10 cri

A ranar Litinin ne shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir da takwaransa na kasar Eritrea Isaias Afwerki, suka yi wata ganawa a asirce a Port Sudan, babban birnin jihar Bahar asawad, inda suka lashi takwabin aiki tare don bunkasa dangantakar da ke tsakaninsu.

Jakadan kasar Sudan a kasar Eritrea Magid Osman, ya shaidawa manema labarai cewa, shugabannin biyu sun yi tattaunawa mai armashi kan batutuwan da za su karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Ya ce, shugabannin biyu sun kuma amince su daidaita batutuwan da suka shafi kasa da kasa da na shiyya-shiyya tare da jaddada da cewa, ko wace kasa tana da manufofinta na kanta da kuma matsayinsu a matsayin kasa.

Bugu da kari, tattaunawar ta yi bitar batutuwa da suka shafi tattalin arziki, siyasa da jin dadin jama'a da kuma abubuwan da ke faruwa yanzu haka a yankin kusurwar Afirka.

A ranar Lahadi ne shugaba Afwerki na kasar Eritrea, ya isa kasar Sudan don ziyarar aiki ta kwanaki 3 tare da halartar bikin baje kolin harkokin yawon shatakawa da sayayya karo na 7 da suka kaddamar tare da shugaba al-Bashir na Sudan a garin Port Sudan. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China