Ministan lafiya na Najeriya Onyebuchi Chukwu ne ya bayyana hakan yayin taron nazarin hadin gwiwa da hukumar lafiya ta duniya ta shirya, inda ya ce gwamnati ita kadai ba za ta iya biyan bukatun lafiyar jama'a ba, don haka wajibi ne sai an yi hadin gwiwa tsakanin sassan masu zaman kansu, kungiyoyin da ba na gwamnati ba, al'umma da kuma abokan hulda domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen yaba wa hukumar lafiya ta duniya da dukkan abokan huldar gwamnatin Najeriya, a kokarin da ta ke yi na inganta sashen ta na lafiya a dukkan matakai.
Chukwu ya ce WHO ta yi nazarin rahoton yadda aka aiwatar da sakamakon taron hadin gwiwar na shekarar 2003-2013, inda ya ce, gwamnati tana da tabbacin cewa, bayanan za su taimaka wajen inganta tsarin kula da lafiya na Najeriya.
A jawabinsa shugaban tawagar hukumar lafiya ta duniya Gama Vaz, ya yaba wa tsare-tsaren Najeriya game da hadin gwiwar cikin shekaru 5 da suka gabata, yana mai cewa, an tsara su ta yadda za su kara inganta hadin gwiwa da kuma shirye-shiryen ta na ilimantar da jama'a game da harkokin kiwon lafiya. (Ibrahim)