Shugaban Jam'iyyar ta kasa Ahmad Adamu Mu'azu ya sanar da hakan a Abuja bayan ganawar sirri da ya yi da 'yan majalissar wakilan jam'iyar. Yana mai bayanin cewa tikitin zarcewa kai tsaye ana ba da shi ne ga jam'iyyun da ba sa bin tsarin demokradiya.
Ahmadu Mu'azu ya ce, jam'iyar PDP an kafa ta ne bisa demokradiya, don haka tsarin za ta bi kuma wadanda suka cancanta lallai za su samu zarcewa.
Yana mai bayyana cewa ba shi da masaniyar cewar tsohon shugaban jam'iyar Bamanga Tukur ya yi ma 'ya'yan jam'iyar alkawari na ba su tikitin zarcewa a zabe mai zuwa.
Za'a dai yi babban zabe na kasar Nigeriya da ta fi yawan al'umma a Nahiyar Afrika a ranar 14 ga watan Fabrairun shekara mai zuwa na 2015. (Fatimah Jibril)