0125murtala
|
Wannan bayanin na kunshe ne a wata sanarwar da sakatariyar hukumar INEC Madam Augusta Ogakwu ta bayar a daren jiya jumma'a a birnin Abuja.
Sanarwar ta ce, zabukan gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi za su biyo baya ne a ranar 28 ga watan Fabrairu.
Sa'annan hukumar ta fitar da ranakun zaben gwamna a jihohin Ekiti da Osun da za'a gudanar a wannan shekara. A cewar sanarwar za'a gudanar da zaben gwamnan jihar Ekiti a ranar 21 ga watan Yunin wannan shekara, yayin da na jihar Osun zai gudana a ranar 9 ga watan Agusta na shekara ta 2014.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.