Shugaban kwamitin tsaro na majalisar dattawan kasar George Sekibo, ya shaidawa manema labarai cewa, an tantance dukkan sunayen da shugaban ya gabatar wa majalisar,abin da ya sa aka tabbatar da nadin nasu.
Shi ma mataimakin shugaban majalisar dattawan Ike Ekweremadu ya tabbatar da nadin jami'an,inda ya yi kira a gare su da su yi amfani da kwarewarsu yayin gudanar da ayyukansu, ta yadda za su gamsar da daukacin 'yan Najeriya.
Idan ba a manta ba, a ranar 16 ga watan Janairu ne shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya kori dukkan manyan hafsoshin sojojin kasar tare da maye gurbinsu da wasu sabbin kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
'Yan Najeriya sun yi imanin cewa,canjin da shugaban ya yi,zai taimaka wajen yaki da ayyukan ta'addanci a kasar.(Ibrahim)