in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A karo na biyu gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin karatun dalibai 502 domin karo ilmi a kasashen waje
2014-01-19 15:25:58 cri

Gwamnatin jihar Kano a arewacin Najeriya ta kashe Naira biliyan 2.8 wajen biyan karatun dalibai `yan asalin jihar su 502 domin karatun digiri na biyu a manyan kasashen duniya daban-daban.

A ranar Alhamis da ta gabata ne gwamnan jihar ta Kano Injinya Rabi`u Musa Kwankwaso ya jagoranci bikin ban kwana ga daliban a fadar gwamnatin jihar.

Wannan dai shi ne karo na biyu da gwamnatin jihar ta Kano ta dauki nauyin dalibai `yan asalin jihar domin karo karato a manyan jami`o'in duniya.

A farkon shekarar bara ne gwamnatin ta tura wasu dalubai 501 domin fadada iliminsu a kasashen Rasha, Malasiya, India, Turkiya, Sudan, Masar da Saudi Arabia.

Dukkannin dalIban dai za su yi karatun digiri na biyu ne a wadannan kasashe.

Da yake jawabi yayin bikin gwamna Rabi`u Musa Kwankwaso ya ce baya ga wadannan dalIbai da ake turawa kasashen ketare, gwamnati tana kashe bIliyoyin Naira wajen daukar nauyin `yan asalin jihar a jami`o'i masu zaman kansu dake sassa daban daban na tarayyar Najeriya domin samun ilimin digiri na daya da na biyu.

Injinya Rabi`u Musa Kwankwaso ya tabbatarwa taron cewa a cikin watan Satumba na wannan shekara ce rukunin farko na dalibai 501 za su kammala karatunsu, amma yanzu haka ma wasu daga cikin irin wadannan dalibai sun samu aiki da wasu kungiyoyi na kasashen duniya, yayin da wasunsu kuma sun ci gaba da fadada iliminsu.

Ko da yake gwamnan, ya ce makasudin tura wadannan dalibai waje domin karo ilimi shi ne domin bayan sun kammala su dawo don koyarwa a jami`o'i mallakar gwamnatin jihar da wasu manyan makarantun gaba da sakandire guda 21 da gwamnatin jiha ta kirkiro.

To amma duk da haka kamar yadda gwamnan ya fada cewa gwamnati da al`ummar jihar Kano za su yi alfahari da ganin `yan asalin jihar na aiki a sassan duniya daban daban.

A sabo da haka gwamnan ya bukaci irin wadannan dalibai da su jajirce tare da zamowa jakadun jiha na gari a duk inda suka je, tare da tabbatar masu da cewa za a rinka bibiyar su a kai a kai domin tabbatar da ganin ba sa wasa.

Shi ma da yake nasa jawabin yayin bikin, gwamnan jihar Niger Alhaji Babangida Aliyu wanda ya samu wakilcin kwamashinan ilimi na jihar Alhaji Dalladi Umar Abdulhamid cewa ya yi hakika abun da gwamnatin jihar Kano ke yi a fagen ilimi abu ne mai kyau wanda ya kamata dukkannin jahohin arewa su yi koyi.

Ya ce lokaci ya yi da gwamnatocin arewacin Najeriya za su rinka alkinta dinbun albarkatun da Allah ya hore masu wajen kyautata rayuwar al`umominsu, ta hanyar ba su ilimi da samar masu da ababen more rayuwa. (Garba Abdullahi Bagwai)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China