A Asabar da ta gabata, an yi liyafa a karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake birnin Ikko na tarayyar Najeriya domin murnar sabuwar shekara tare da jinjinawa sabon karamin jakadan kasar Sin, mista Liu Kan.
Bikin ya samu halartar wasu jami'an gwamnatin kasar Najeriya da suka hada da wakilan gwamnonin jihohin Lagos da Ogun, mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Lagos , da wakilan sassan masana'antu, hada-hadar kudi, al'adu, ilimi, da yada labaru na wurin. Har ila yau jama'a da suka hada da wakilan Sinawan mazauna birnin na Ikko, da na kamfanonin kasar Sin, da kafofin yada labarun kasar, baki daya fiye da 200 suka halarci bikin.
Sabon karamin jakadan kasar Sin a birnin Ikko, mista Liu Kan a jawabinsa a wajen bikin, ya waiwayi nasarorin da kasashen Sin da Najeriya suka samu a fannonin ayyukan bunkasa tattalin arziki da cinikayya, da musayar al'adu. Yana mai cewa, a matsayin karamin jakadan kasar Sin na 5, zai yi kokari tare da Sinawa dake karkashin kulawarsa, da kamfanonin kasar Sin dake wurin, da kuma ma'aikatan ofishin jakadanci, domin kara habaka hadin gwiwar kasashen 2 zuwa fannoni daban daban.
A cewarsa zai yi haka ne bisa goyon bayan da hukumomin kasar Najeriya da jama'ar kasar abokan kasar Sin suke masa. (Bello Wang)