in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ofishin jakadancin Sin dake Najeriya yayi liyafar ban kwana ma jakada Deng Boqing da uwargidar sa
2014-01-17 10:32:54 cri


Ranar Alhamis 16 ga wata da dare ne, a cibiyar al'adun kasar Sin dake Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, ofishin jakadancin Sin dake kasar ta shiya liyafar ban kwana ma jakada Deng Boqing da uwargidarsa Madam Cheng Hong.

Daukacin ma'aikatan ofishin jakadancin Sin dake Najeriya, da ministan kula da harkokin al'adu, yawon shakatawa da gyara halayen 'yan kasa na Najeriya Mista Edem Duke, da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijan kasar malam Ibrahim Mantu, da jami'an diflomasiyya daga sauran kasashe sun halarci liyafar.

A cikin jawabin da ya gabatar, jakada Deng Boqing ya ce, a cikin tsawon wa'adin aikinsa na shekaru uku a Najeriya, ya ganema idanunsa yadda Najeriya ta bunkasa cikin sauri, ko a fannin tattalin arziki, ko a fannin zamantakewar al'umma, ko kuma a fannin ababen more rayuwar jama'a. Haka kuma, Najeriya na kara taka rawar a-zo-a-gani a cikin batutuwan ECOWAS da kuma kungiyar tarayyar Afirka.

Game da huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Najeriya, Mista Deng Boqing ya ce, a cikin 'yan shekarun nan, dangantakar kasashen biyu na habaka cikin sauri a fannonin da suka hada da siyasa, tattalin arziki, kasuwanci, kimiyya da fasaha, al'adu da sauransu, kuma jama'ar kasashen biyu na kara samun fahimtar juna tsakaninsu.

Mista Deng ya ce, duk inda zai tafi nan gaba, ba zai manta da Najeriya da al'ummarta ba, kuma zai ci gaba da ba da gudummawa gwargwadon karfinsa wajen raya dangantakar kasashen Sin da Najeriya.

Sai dai cif Edem Duke, da malam Ibrahim Mantu da sauran wasu jami'an gwamnatin Najeriya sun yabo kwarai bisa ga aiki tukuru da jakada Deng Boqing da matarsa Madam Cheng Hong suka yi, wajen inganta hadin-gwiwa da mu'amala tsakanin Sin da Najeriya, kuma suna sa ran jakada Deng da matarsa za su samu karin ci gaba a nan gaba.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China