kakakin hukumar kula da harkokin 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) Adrian Edwards ne ya bayyana hakan a jiya Jumma'a 13 ga wata, yayin wani taron 'yan jarida da aka shirya a birnin Geneva.
Mista Edwards ya ce, bisa alkaluman da kungiyar Red Cross ta kasar, da hukumar jin kai ta Denmark suka fitar, mutane sama da 450 ne suka mutu sakamakon rikicin da ya abku a birnin Bangui, hedkwatar kasar, yayin da wasu mutane sama da 160 suka mutu a sauran sassan kasar daban daban.
Dadin dadawa, mista Edwards ya kara da cewa, mutane kimanin dubu 159 sun tsere daga gidajen su sakamakon tashe tsahen hankulan da suka auku cikin makon jiya, yayin da wasu al'ummar kasar kimanin 1800 suka tsallaka zuwa Kongo Kinshasa da kuma Congo-Brazzaville domin tsira da rayukan su.(Fatima)