Mr Hong ya sanar da hakan ne a ganawar da ya yi da manema labarai wanda aka saba yi duk rana a nan birnin Beijing, fadar gwamnatin kasar, lokacin da aka bukaci ya yi bayani game da sahihancin zaben shugaban kasar ta Madagascar.
Kotu ta musamman game da zaben Shugaban kasar ta Madagascar a ranar Jumma'ar da ta gabata ne ta sanar da sunan Hery Rajaonarimampianina a matsayin wanda ya lashen babban zaben shugaban kasar a zagaye na biyu da aka yi a ranar 20 ga watan Disambar bara da kashi 53.49 a cikin 100 abin da ya nuna ya doke abokin hamayyarsa Jean Louis Robinson.
Mr Hong ya ce kasar Sin tana fatan Madagascar za ta kawo karshen rikicin siyasarta sakamakon wannan zabe, sannan ta samu daidaituwar kasar da ci gaba mai dorewa. (Fatimah)