in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarwarin da bangarorin da ke rikici da juna a kasar Sudan ta Kudu suke yi ya shiga wani mawuyacin hali
2014-01-22 17:16:47 cri

Rahotanni daga gwamnatin kasar Sudan ta Kudu, na cewa, shugabannin kasashen gabashin Afirka da shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir za su je birnin Juba, babban birnin kasar Sudan ta Kudu a ran 23 ga wata, inda za su yi shawarwari da shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir, don daidaita mawuyacin halin da shawarwarin da ake yi a tsakanin bangarorin Sudan ta Kudu da ke rikici da juna ya shiga . A sa'i daya kuma, ministan watsa labaru na kasar Sudan ya bayyana cewa, Mista al-Bashir zai taimaka matuka wajen sulhunta bangarorin da ke rikici da juna a kasar Sudan ta Kudu.

Kafin haka, yawancin kasashen duniya suna sa ran ganin shawarwarin da kungiyar raya gwamnatocin gabashin kasashen Afirka take jagoranta a tsakanin bangarori biyu da ke rikici da juna a kasar Sudan ta Kudu zai yi nasara,inda galibin kasashen duniya ke ganin cewa, shawarwarin za su zama mataki na farko na kawo karshen rikicin da ake fama da shi a Sudan ta Kudu. Amma tun bayan da aka kaddamar da shawarwarin a hukunce a birnin Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha a farkon watan nan har zuwa yanzu, ba a samu wani ci gaban da a zo a gani ba, hakika yanzu shawarwarin sun shiga cikin wani mawuyacin hali. Akasarin jama'a na bayyana ra'ayin cewa, babban sabanin da ke tsakanin bangarorin biyu shi ne matsalar sakin fursunonin siyasa. Yayin da aka fara tashe-tashen hankula da makamai a kasar Sudan ta Kudu a shekarar bara, nan da nan shugaban kasar Salva Kiir ya ba da umurnin kama wasu manyan jami'ai 11 da ake tuhuma da yunkurin juyin mulki, wadanda har zuwa yanzu ba a sake su ba. A 'yan kwanakin baya, shugaba Kiir ya yi nuni da cewa, ana yin shawarwari a kokarin yiwa fursunonin siyasar afawu. Dangane da batun,masu nazarin harkokin siyasa na ganin cewa, yayin ganawar da shugabannin kasashen gabashin Afirka za su yi da shugaba Kiir a ran 23 ga wata, mai yiyuwa ne za a mataswa shugabannin Sudan ta Kudu lamba kan batun sakin fursunonin siyasan da suke rike da su.

Tun lokacin da aka fara tashe-tashen hankula da makamai a tsakiyar watan Disamban shekarar bara har zuwa yanzu,al'amura sai kara rincabe wa suke yi a Sudan ta Kudu, a halin yanzu mutane fiye da dubu ne suka mutu yayin da fiye da dubu goma suka yi gudun hijira. A 'yan kwanakin baya, sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu sun sanar da cewa, sun sake kwace garin Malakal mai arzikin man fetur, wanda ya taba fada wa hannun dakarun da ke adawa da gwamnati na tsawon kusan wata guda. Kafin haka kuma, sojojin gwamnatin sun sanar da cewa sun sake kwace birnin Bor mai arzikin man fetur, babban birnin jihar Jonglei. Sake samun garin Malakal da sojojin gwamnatin suka yi,ya shaida cewa, sojojin gwamnati sun maido da ikonsu a dukkan manyan birane da garurrun jihohin biyu. Amma wasu rahotanni sun bayanna cewa, a kauyuka da yawa na kasar Sudan ta Kudu, dakarun da ke adawa da gwamnati ne suke da karfi sosai, sakamakon haka ne, ake ci gaba da rikici a kasar. Rahoton da MDD ta bayar a 'yan kwanakin baya ya nuna cewa, dukkan sassan biyu sun aikata laifukan kisan gilla da cin zarafin mata da sauran ayyukan nuna karfin tuwo a kasar Sudan ta Kudu a halin yanzu.

Ya kara da ziyararsa ta wannan karo, a cikin wata guda kacal, shugaban kasar Sudan al-Bashir ya je kasar Sudan ta Kudu sau biyu,don sulhuntawa. A 'yan kwanakin baya, ministan watsa labaru na kasar Sudan Ahmed Bilal ya gaya wa manema labaru cewa, Bashir yana da wata kyakkyawar dangantaka da takwaransa na kasar Sudan ta Kudu Mista Salva Kiir, sabo da haka Bashir zai iya taimakawa wajen sa kaimi don a saki fursunonin siyasan da ake tsare da su da sauran batutuwa da ke hana ruwa gudu a rikicin na Sudan ta kudu, wannan ya sanya Bashir ya zama mutumin da ya fi kwarewa wajen daidaita mawuyacin hali da shawawarin Sudan ta kudun ke ciki a halin yanzu, ban da wannan kuma, Bashir da shugabannin dakarun da ke adawa da gwamnati sun san juna, sabo da haka ana ganin nan ma al-Bashir na iya ba da shawara ga shugabannin da ke adawa da gwamnatin Sudan ta Kudu.

Wasu masu nazarin harkokin yau da kullum suna ganin cewa, ko da yake tun bayan da Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai a shekara ta 2011, kasar Sudan da Sudan ta Kudu su kan samu sabani a dangantakarsu game da man fetur da iyakar kasa da sauran matsaloli, amma samun sulhuntawa a tsakanin bangarorin da ke rikici da juna a kasar Sudan ta Kudu ya dace da moriyar ksar Sudan. Sabo da rikcin Sudan ta Kudu ya sanya 'yan gudun hijira da yawa sun tsallaka zuwa kasar Sudan, wannan ya kawo barazana ga zaman karko a Sudan. Bugu da kari al-Bashir yana da fiffiko kan sauran shugabannin gabashin Afirka a kokarin sulhuntawa a Sudan ta Kudu, ganin yadda a da Sudan da Sudan ta Kudu sun taba zama a matsayin kasa guda, don haka shugaba Bashir ya san bangarorin biyu da ke yaki da juna, ya kuma san yanayin kabilun kasar daban daban, wannan zai kara taimaka masa a kokarin da ya ke yi na sulhunta rikicin kasar Sudan ta kudu.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China