in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kokarin Sin na sa kaimi ga tsagaita bude wuta a Sudan ta Kudu ya dace da moriyar jama'ar kasa
2014-01-09 18:59:27 cri
A yau alhamis 9 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin, madam Hua Chunying ta bayyana a nan birnin Beijing cewa, Sin tana kokarin sa kaimi na ganin an tsagaita bude wuta da dakatar da nuna karfi a Sudan ta Kudu, abin da ya dace da moriyar jama'ar kasar Sudan ta Kudu, tare da ba da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka.

Game da kokarin da Sin take yi wajen shiga tsakani kan batun Sudan ta Kudu, wasu kafofin yada labaru na kasashen waje sun bayyana cewa, Sin tana haka ne saboda kasar Sudan ta Kudu tana da albarkatun man fetur da dama. Game da zancen Madam Hua ta yi bayanin cewa Sin tana kokarin sa kaimi ga yin shawarwari tsakanin bangarorin biyu dake rikici da juna don haka ko kadan zargin da ake yi bai dace da ka'idar da Sin take bi ba na kin tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na sauran kasashen duniya ba.

Madam Hua ta sake bayyana cewa, Sin ba za ta sa hannu cikin harkokin cikin gida na sauran kasashen duniya ba domin wannan muhimmin abu ne dake cikin manufofin kasancewa tare cikin lumana guda biyar.

Sin a tsaye take tsayin daka tare da gudanar da manufofin yadda ya kamata. A matsayin wata zaunanniyar memba ta kwamitin sulhu na MDD, kana babbar kasa mai dauke da alhaki a duniya, tun asali Sin tana kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, abinda ya sa ta taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga tabbatar da zaman lafiya da tsaro da bunkasuwa a nahiyar Afirka cikin dogon lokaci, in ji madam Hua.

Ban da haka, madam Hua ta kara da cewa, Sin tana hadin gwiwa da wasu kasashe a fannin makamashi da sauransu, domin taimaka musu wajen bunkasa tattalin arziki da kyautata rayuwar jama'arsu, wannan ya dace da moriyar jama'a a wurin. A sabili da haka, Sin za ta ci gaba da ba da gudummowa wajen sa kaimi ga tabbatar da zaman lafiya da tsaro da bunkasuwa yadda ya kamata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China