Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ne ya bayyana hakan ranar Talata, yayin da yake bayani ga manema labarai game da yadda aka kammala matakin farko na aikin jigilar makamai masu guba na kasar ta Syria.
Hong Lei ya ce, gwamnatin Syria ta aiwatar da shawarwarin kungiyar haramta amfani da makamai masu guba ta duniya (OPCW) da kudurorin MDD yadda ya kamata, ta hanyar kammala zagayen farko na jigilar makamanta masu guba ranar Talata da ta gabata.
Ya ce sauran kasashe ciki har da Sin, Rasha da Denmark, hakika sun taka rawa don tabbatar da cewa, aikin ya gudana lami lafiya.
Mr. Hong ya ce, aikin jigilar makamai masu guba, wani muhimmin mataki na kaiwa ga lalata su, kuma kasar Sin za ta hada kai da sauran bangarori don ganin abubuwa sun gudana kamar yadda aka tsara. (Ibrahim)