in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana goyon bayan kasashen dake yanki daya da Syria don su taka rawa a kokarin daidaita matsalar kasar
2014-01-20 21:55:53 cri
Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya furta a ranar Litinin 20 ga wata cewa, hanyar siyasa ita ce hanya kadai da za a bi don daidaita batun Syria, kana kasar Sin a nata bangaren tana mai da hankali kan rawar da wasu kasashen dake yanki daya da Syria suke taka a kokarin daidaita matsalar kasar, gami da nuna musu goyon baya.

Kafin haka kungiyar adawa ta kasar Syria NCSROF ta ce, ba za ta halarci taron Geneva na biyu kan batun Syria ba, sai dai idan MDD ta soke gayyatarta ga kasar Iran don ita ma ta shiga cikin taron Geneva da za a kira.

Dangane da batun, Hong Lei ya bayyana cewa, kamata ya yi bangarorin kasar Syria su bayyana ra'ayoyinsu yayin shawarwari. A cewarsa, kasar Sin na kira ga bangarorin kasar da su nuna yakini wajen halartar taron Geneva karo na 2, tare da sa hannu kan sanarwar Geneva da kokarin aiwatar da ita.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China