Babbar kungiyar adawa ta Syria NCSROF ta sanar a ranar Litinin 20 ga wata cewa, ba za ta halarci taron Geneva na 2 dangane da batun Syria ba, sai dai idan MDD ta soke gayyatar da ta ba kasar Iran, ko kuma idan Iran ta amince da sanarwar taron Geneva na farko.
A cikin sanarwar da Louay Safi, kakakin kungiyar NCSROF ya fitar ya ce kungiyar za ta shirya wani taron manema labaru musamman ma a kan batun.
Kafin haka, kunigyar NCSROF ta sanar a Istanbul na kasar Turkiya a ranar Asabar 18 ga wata cewa, za ta halarci taron Geneva na 2 da zai gudana a ranar 22 ga wata. (Bello Wang)