A wannan rana da karfe 10 na safe, bayan jirgin ruwa na Yan Cheng ya isa tashar jiragen ruwa ta Limassol, ministan tsaron kasar Cyprus Photis Photiou da kuma jakadan kasar Sin dake kasar Liu Xinsheng sun tarbi jirgin ruwan Yan Cheng da zuwansa a wannan tashar ruwan.
Mr. Photiou ya bayyana cewa, ya yi maraba da zuwan jirgin ruwan soja na kasar Sin a kasarsa karo na farko. Kuma yayin da ya tsokaci kan aikin jigilar makamai masu guba na kasar Syria, ya nuna cewa, kasar Cyprus ta tsaya tsayin daka wajen nuna goyon baya ga kasashe da MDD dake dukufa kan wannan aiki.
Jiragen ruwan soja na kasashen Norway da Danmark sun kama hanyar zuwa Syria a ran 3 ga wata, domin jigilar da makamai masu guba daga kasar Syria da za a lalata, bisa kudurin MDD da abin da ya shafa. (Maryam)