Yayin taron manema labaran da aka yi a wannan rana, ministan ya bayyana cewa, manyan shugabannin kasar sun tsai da shawara kan halartar taron Geneva karo na biyu, don nuna matsayin kasar wajen warware batun Syira ta hanyar zaman lafiya.
Ya kuma kara da cewa, kasar za ta dukufa wajen nuna goyon baya ga manzon musamman mai kula da batun Syira na MDD da kungiyar tarayyar kasashen Larabawa, Lakhdar Brahimi. Baya bayan nan, shugaban kasar Algeria ya yi shawarwari da Mr. Brahimi kan batun Syria, inda shugaban kasar ya bayyana cewa, zai dukufa wajen ciyar da shawarwarin dake tsakanin kasashen Larabawa da bangarorin kasar Syria da abin ya shafa gaba.
Haka zalika, ya jaddada cewa, taron Geneva karo na biyu zai ba da taimako ga bangarorin daban daban da abin ya shafa na kasar Syria wajen daukar alhakinsu yadda ya kamata kan kasarsu da kuma jama'arsu. (Maryam)