Shugabar kwamitin tarayyar Afrika AU, Nkozasana Dlimini-Zuma, ta yi kira ga bangarori masu gaba da juna a kasar Sudan ta Kudu da su cimma yarjejniyar dakatar da bude wuta, in ji wata sanarwar da kungiyar ta fitar a ranar Talata.
Jami'ar ta yi wannan kira a yayin wata ziyarar aiki da ta kai a Juba, hedkwatar kasar Suda ta Kudu. A tsawon wannan ziyara, madam Dlamini-Zuma ta gana da shugaban Sudan ta Kudu Salvar Kiir Mayardit, da wasu fursunoni da ake zargi da yunkurin juyin mulki.
Madam Dlamini-Zuma ta jaddada muhimmancin kwamitin bincike kan abubuwan da suka faru a kasar Sudan ta Kudu, da kwamitin zaman lafiya da tsaro ya bukaci a kafa shi tun ranar 30 ga watan Disamban da ya gabata, nada manufar ganin an kyautata halin mutanen da fama da azabar gallazawa da keta hakkin dan adama da kuma taimakawa gwamnatin Sudan da Kudu gano da muhimman hanyoyin da za su karfafa karfin hukumomin kasar, tare da ba da damar sasantawa.
Duk da cewa bangarorin dake gaba da juna sun yi bayani kan manyan dalilan da suka janyo rikicin da kasar take fama da shi a halin yanzu, sun amince cewa, matsala ce ta siyasa a cikin jam'iyyar dake mulki, da ya kamata a warware ta hanyar siyasa maimakon amfani da karfin soja, in ji sanarwar AU.
Haka kuma sanarwar ta AU, ta nuna cewa, bangarorin dake gaba da juna na da ra'ayi guda na sanya hannu kan wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta cikin gaggawa ba tare da wani sharadi ba. (Maman Ada)