Hukumar shirin samar da abinci ta MDD wato WFP a ranar Litinin din nan 13 ga wata ta kaddamar da shirin ba da agajin gaggawa na abinci na tsawon watanni uku domin ba da taimakon jin kai ga wadanda fadan kasar Sudan ta Kudu ya rutsa da su.
Darektan hukumar mai kula da yankunan gabashi da tsakiyar Afrika Valerie Guarnieri ta ce, kudi dalar Amurka miliyan 57.8 na agaji da aka samu, za'a yi amfani da su ne ga wadanda suka rasa muhallansu a kasar kusan 400,000 domin samar da abinci masu gina jiki musamman ga mata masu jego da kananan yara da suke fuskantar tangarda wajen abin da za su ci.
Hukumar kuma ta yi allawadai da satar kayayyakin abincinta da wadansu ke yi, tana mai cewa, kayayyakin abincin da aka tanada a cibiyoyi kusan 100 a sassa daban daban na kasar suna fuskantar barazana.
Mataimakin darektan hukumar a kasar Sudan ta Kudun, Eddie Rowe ya yi kira ga dukkan bangarori dake arangama da juna da su kare lafiyar fararen hula da kuma kayayyakin agaji da aka tanada kamar abinci, saboda a samu amfani da su lokacin da ake da matukar bukata, musamman ga mata da yara da tashin hankalin ya rutsa da su.
Hukumar shirin samar da abincin ta MDD har ila yau tana taimakawa dubun dubatan 'yan gudun hijira da suka tsallaka kan iyakar kasar zuwa makwabtansu kamar kasashen Uganda, Habasha da kuma Kenya. (Fatimah)