Tawagar wanzar da zaman lafiya na MDD tana tsaurara matakan tsaro a sansanoninta dake fadin kasar Sudan ta Kudu domin ba da kariya yadda ya kamata ga 'yan gudun hijira dake ciki su 65,000, in ji kakakin majalissar a ranar Alhamis din nan.
Farhan Haq, a lokacin zantawa da manema labarai da aka saba yi duk rana ya ce, daga cikin matakan tsaron da aka dauka su ne binciken makamai da kuma hadin gwiwwa tsakanin 'yan sandan majalissar da sojoji masu gadi a ciki da wajen wannan unguwanni.
Binciken makamai, in ji shi, ana yin su a dukkan sansanoni da suka hada da na babban birnin kasar Juba da kuma Bor a jihar Jonglei, Bentiu a jihar Unity da Malakal a jihar Upper Nile kamar yadda bayanin ya fito daga tawagar majalissar dake Sudan ta Kudu UNMISS.
An riga an gina katangun kariya da kuma shingaye, sannan duk wadanda suke zo wajen don neman mafaka, sai an binkice su gaba daya, haka kuma wadanda za su fita. Sannan tawagar na kokarin kara wassu matakan tsaron domin inaganta yanayin sansanonin.
Akwai karin 'yan sanda majalissar guda 63 da suka iso a ranar Laraban nan da ta gabata, adadin da yanzu ya kai 315, in ji tawagar majalissar. (Fatimah)