Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta yi Allah wadai da babbar murya game da kisan sojojin MDD a kasar Sudan ta Kudu.
A cikin wata sanarwarta ta ranar Alhamis, AU ta bayyana cewa, Nkosazana Dlamini-Zuma, shugabar kwamitin kungiyar AU, ta samu labari cikin bacin rai kan kisan sojoji biyar dake cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Sudan ta Kudu(MINUSS), tare da wasu fararen hula bakwai dake tawagar aiki, a cikin wani harin kwancin bauna da wasu mutane da ba'a tantance asilinsu ba suka kai a yankin Jonglei na kasar Sudan ta Kudu a ranar 9 ga watan Afrilun shekarar 2013.
Shugabar kwamitin ta yi suka kan wannan hari na rashin imani, in ji sanrawar, haka kuma ta mika ta'aziyar kungiyar AU zuwa ga iyalan wadannan sojojin wanzar da zaman lafiya, da kasashensu, da tawagar MINUSS da kuma MDD.
Haka kuma madan Dlamini-Zuma ta jaddada yabo da sunan kungiyar AU kan namijin kokarin da tawagar MINUSS tare da ba ta kwarin gwiwa na cigaba da ayyukanta duk matsalolin dake fuskanta. (Maman Ada)