in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fada a Sudan ta Kudu zai kara yunwa da karancin abinci, in ji FAO
2014-01-14 10:06:07 cri

Tashin hankalin da ake fuskanta a kasar Sudan ta Kudu yana kawo barazanar yunwa da wahalhalun jama'a, sannan kuma zai kawo karancin abinci, in ji hukumar samar da abinci da aikin noma ta MDD wato FAO.

Hukumar dake da cibiya a birnin Rome da wassu kungiyoyi da ayyukansu ya jibanci hakan suna kokarin neman samun taimakon kudi akalla dalar Amurka miliyan 61 saboda samar da abinci cikin gaggawa da ceto rayuwar al'umman kasar.

Yanayin zamantakewa a kasar ya tsananta matuka tun lokacin da fada ya barke a tsakiyar watan jiya na Disamba, abin da ba kawai ya yi sanadin rasa rayukan mutane da dama ba, har ma ya sa da yawa sun rasa muhallinsu, sannan ya kawo koma baya ga harkokin abinci da jin kai da kuma rashin tabbas na makomar wadanda suka rage a cikin kasar.

Wakiliyar hukumar a kasar Sudan ta Kudu Sue Lautze, ta ce, tsara lokaci shi ne komai yanzu a kasar, akwai kifaye a koguna, akwai kuma dabbobi da makiyaya ke kokarin kare su, sannan akwai lokacin shuka na masara, gyada da dawo da za'a yi a watan Maris din nan mai zuwa.

Shi ma a nasa bayanin, babban darekta na sashin ba da agajin gaggawa na hukumar Dominique Burgeon ya ce, ko kafin a fara wannan fadan wanda ya janyo rasa muhallan fiye da mutane 352,000, kusan miliyan 4.4 daman an rigaya an kiyasta cewa, za su fuskanci karancin abinci a wannan shekarar da muke ciki, sannan daga cikin wannan adadi, kusan 830,000 sun rigaya suna fuskantar karancin abinci mai tsanani. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China