A jiya Lahadi 16 ga wata, kasar Sudan ta sanar da amincewarta game da shawarar da kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta ba ta don kawo karshen takaddamar dake tsakaninta da makwabciyarta Sudan ta Kudu.
Kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin kasashen wajenta Abu Bakr Al-siddiq ya bayyana, gwamnati a hukumance ta amince da shawarar kungiyar AU wadda babban kwamitin lura da ayyuka a Sudan din ta gabatar, da ta shafi yadda za'a samu matsala a cikin takaddamar da ake yi yanzu haka.
A cikin shawarar, an bukaci kwamitin lura da shirin shata kan iyakoki na AU da ya hada wata tawagar da za ta tantance iyakokin da bai kamata a zuba sojoji ba a kasar, kamar yadda kasashen biyu suka gabatar ma kwamitin tun da farko.
Haka kuma shawarar ta bukaci a shigar da shirin tantance kan iyakar cikin hadin gwiwar jami'an tsaron kasashen biyu tun daga ranar 18 ga watan Yunin bana zuwa nan da makonni 6 masu zuwa, in ji kakakin.
Al-siddiq ya ce, kwamitin da AU ta gabatar zai hadu da jami'an tsaron hadin gwiwa da na siyasa na kasashen biyu domin sanar da sakamakon tantancewarsu tare.
Ana dai zaman dar dar ne tsakanin kasashen biyu bayan da shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir ya sanar da dakatar da fitar da man fetur ta yankin kasarsa a watan da ya gabata bisa zargin da Khartoum take ma Juba cewa, ita ce ke ingiza 'yan tawaye a kan kasar ta Sudan.
A ranar Alhamis din da ya gabata ne AU ta sanar da shawarar da ta mika ma kasashen biyu domin kawo karshen takaddamar da kuma banbancin ra'ayi na zancen fitar da man fetur tsakanin kasashen biyu. (Fatimah)