in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutum 1 ya mutu sannan da dama sun ji rauni a sansanin MDD dake Sudan ta Kudu
2014-01-16 16:25:39 cri

Kakakin MDD Martin Nesirky a ranar Laraban nan ya tabbatar da cewa, an hallaka mutum daya, sannan da dama suka samu raunuka, ciki har da sojan majalissar guda daya, lokacin wani hari da aka kai wa sansaninta dake arewacin kasar Sudan ta Kudu.

Da yake bayani game da hakan, Mr. Nesirky ya ce, bayanai daga ofishin wanzar da zaman lafiya na majalissar a kasar sun ce, ana cikin wani hargitsatsen yanayi a Malakal, babban birnin jihar Upper Nile bayan harin da aka kai wajen ranar Talata.

Kakakin ya yi bayanin cewa, sai da jami'an wanzar da zaman lafiya suka yi ta harbi a sama domin kare 'yan gudun hijira da ke cikin sansani da kuma tsoratar da duk wadanda suke fada da juna matsowa kusa da harabarsu.

Duk da cewar, fada ya dan sassauta, an ji karar harbin bindigogi a garin na Malakal da kuma kusa da sansanin Bor wanda ya ba da matsuguni ga mutane sama da 9,000, sannan kuma akwai karin 6,000 dake neman mafaka a sansanin majalissar dake Bentiu. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China