in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECOWAS ta yi hasashen samun bunkasuwa da kashi 7,1 cikin 100 a shiyyar bana
2014-01-08 15:09:32 cri

Kungiyar tattalin arzikin yammacin Afrika ECOWAS ta yi hasashen samun bunkasuwar tattalin arziki da kashi 7,1 cikin 100 a shiyyar yammacin Afrika a shekarar 2014, a cewar wasu alkaluman da aka fitar a ranar Talata.

Hasashen ya karu bisa ga shekarar 2013 dake kashi 6,3 cikin 100 da kuma na shakarar 2012 dake kashi 6,6 cikin 100, in ji sanarwar mista Sunny Ugoh, mataimakin darektan harkokin sadarwa na kungiyar ECOWAS.

Alkaluma sun nuna cewa, Sierra Leone za ta samu bunkasuwa mafi girma da kashi 14,6 cikin 100 a yayin da kasar Cap Vert za ta samu bunkasuwa mafi kankanta da kashi 0,5 cikin 100.

Wasu kasashe shida da suka hada da Burkina Faso, Najeriya, Ghana, Liberiya, Cote d'Ivoire da Sierra Leone sun kasance cikin kasashen da za su zarce adadin bunkasuwar tattalin arziki mafi girma da kashi 6,3 cikin 100 kamar yadda kungiyar ECOWAS ta yi hasashe, a cewar wannan sanarwa.

Cigaban zai shafi fannonin samar da gas, man fetur da sauran ma'adinai da ma fannin noma, in ji wannan sanarwa.

Haka kuma an nada shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou da takwaransa na kasar Ghana John Dramani Mahama a matsayin wakilan da za su ido kan shirin kungiyar ECOWAS na amfani da kudi daya, in ji wannan sanarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China