Kwamandan tawagar Zhang Geqiang ya bayyana cewa, ma'aikatan da za su yi aikin wanzar da zaman lafiya za su kashe tsawon watanni 8 a kasar ta Mali, inda za su bayar da gudummawa ga aikin shimfida zaman lafiya a kasar da kuma sake farfado da tattalin arzikin kasar.
Baya ga wannan tawaga, kasar ta Sin ta kuma tura dakarun kiyaye zaman lafiya zuwa kasahen Liberia, Sudan, Jamhuriyar demokiradiyar Congo, Sudan ta Kudu da Lebanon.
Idan ba a manta ba, a watan Disamba ma, kasar Sin ta tura rukuni na farko na ma'aikatan kiyaye zaman lafiya, wanda ya kunshi sojoji, masu aikin gadi da ma'aikatan lafiya zuwa kasar ta Mali. (Ibrahim)