Ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian ya bayyana a ran 19 ga wata cewa, a 'yan kwanakin baya sojojin Faransa sun inganta matakan soja da suke dauka a kokarin su na yaki da ta'addanci da dakile ayyukan wani sashen kungiyar Al-Qaeda dake arewacin Mali.
Le Drian wanda ya bayyana hakan ga kafar radio ta "Europe 1", ya kara da cewa sojojin kasar ta Faransa sun samu wasu nasarori a wannan aiki.
Ministan ya ce, yanzu sojojin Faransa suna tsare da Mokhtar Belmokhtar, wanda ya tsara shirin sace mutanen da aka yi garkuwa da su, aka kuma kashe su a wani filin hakar iskar gas da ke yankin In Amenas na kasar Aljeriya, da ma mambobin wasu sauran kungiyoyi masu ra'ayin ga-ni-kashe-ni. Ya ce, a shekara ta 2014 mai zuwa sojojin Faransa za su ci gaba da yaki da masu ra'ayin ga ni-kashe-ni dake kasar ta Mali.
Har wa yau wata kafar watsa labaru ta Faransa ta ruwaito Jean-Yves Le Drian ta bakin mashawarcin sa na cewa, sojojin Faransa za su kasance a Mali tsawon lokaci nan gaba, domin ci gaba da yaki da masu ra'ayin rikau ciki hadda wadanda suka zo daga kasashen waje. (Danladi)