Sojojin kiyaye zaman lafiya na Sin dake Mali za su karfafa matakan tsaro yayin zaben majalisa
Jiya Asabar 14 ga wata bisa agogon wuri, an kai wani harin kunar bakin wake a ginin bankin raya kasar ta Mali dake birnin Kidal, wanda ya haddasa mutuwar sojojin kiyaye zaman lafiya guda biyu, yayin da guda bakwai suka jikkata.
Kuma Yau Lahadi 15 ga wata, an gudanar da zaben majalisar dokokin kasa zagaye na biyu a Mali, sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin dake kasar Mali sun riga sun karfafa matakan tsaro zuwa wani babban mataki don kiyaye yanayin zaman lafiyar zaben. (Maryan)