Ofishin tsare-tsare na hukumar ba da agajin jin kai ta MDD OCHA, ya bayyana damuwar da gamayyar kungiyoyin ba da agaji ke nunawa, don gane da mawuyacin halin da kasar Afirka ta Tsakiya CAR ta fada.
Rahotannin baya bayan nan sun jiyo jami'i mai magana da yawun MDDr na cewa, halin dar dar da ake ciki a birnin Bangui da kewaye, na barazana ga burin da ake da shi, na tsaron rayukan fararen hula.
A wani ci gaban kuma asusun yara na MDDr UNICEF, ya bayyana damuwa ga tabarbarewar yanayin tsaro a kasar, matakin da ke dada jefa yaran kasar cikin mawuyacin halin rayuwa, da karancin abinci mai gina jiki.
Tun farkon watan nan da muke ciki ne dai al'ummun kasar mabiya addinin kirista da musulmi, ke kaiwa junan su hare-hare a birnin na Bangui da kewaye, lamarin da ya haddasa kisan fararen hula akalla 450, baya ga mutane kusan 160,000 da balahirar ta raba da gidajensu.
Wata kididdiga daga hukuma mai lura da harkokin 'yan gudun hijira ta MDD, ta nuna cewa, kimanin kaso 43 bisa dari na daukacin al'ummar Afirka ta Tsakiya na bukatar tallafin jin kai. (Saminu)