in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta nuna damuwa kan tabarbarewar matsalar jin kai a CAR
2013-12-17 10:58:21 cri

Wasu cibiyoyin MDD da dama ne suka bayyana damuwarsu a ranar Litinin gaban tabarbarewar rikici a kasar Afrika ta Tsakiya CAR, inda miliyoyin fararen hula suke cikin barazanar matsalar karancin abinci tare da cigaban tashe-tashen hankali.

A cikin dogon lokaci, an kasa mai dai hankali kan rayuwar kananan yara a Afrika ta Tsakiya, balantana daukar matakai a cikin wannan riciki, in ji darekta janar na asusun MDD game da kananan yara (UNICEF), Anthony Lake da ya kimanta kasha-kashe da cin zarafin yara da wani abin kunya ga duniya.

Rikicin Afrika ta Tsakiya ya rutsa a halin yanzu da yara miliyan 2,3. An kashe yara da dama dalilin kasancewarsu musulmai ko kristoci. Kuma an tilastawa daruruwan yara kaura daga gidajensu domin su boye cikin tsoro domin gujewa mayakan bangarorin biyu. Yara sun shaida ayyukan azabtarwa da na tashin hankali, haka kuma ana sanya kananan yara aikin soja, har yawansu ya kai kusan dubu shida kamar yadda ake kyautata zato, in ji mista Lake a cikin wata sanarwar zuwa ga 'yan jarida.

Har zuwa wannan shekara, UNICEF da sauran kungiyoyin ba da agaji sun yi allura ga yara fiye da dubu 480, 'yan kasa da shekara biyar game da cutar dusa. Mutane fiye da dubu 47 suka bar gidajensu, yawancinsu daga Bossangoa, kuma sun samu taimakon barguna, tantunan roba, sabulu da jarkunan ruwa daga asusun UNICEF. Kuma a halin yanzu mutane kimanin dubu 280 suka samu ruwan sha masu tsabta.

A nata bangare, hukumar MDD ta abinci da noma (FAO) ta tabbatar cewa, miliyoyin jama'a ne suke cikin barazanar matsalar karancin abinci a kasar ta Afirka ta Tsakiya, inda manoman kasar suke bukatar taimakon gaggawa domin hana tabarbarewar wannan matsala. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China