A ranar Laraba 16 ga wata ne Martin Nesirky, kakakin babban sakataren MDD Ban Ki-moon, ya sanarwa manema labarai cewa, ofishin kula da harkokin jin kai na MDD, ya sanar a ranar Laraba cewa, darektocin da ke gudanar da aikin gaggawa na hukumomin MDD da kungiyoyi masu zaman kansu, za su fara wata ziyara a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya CAR a ranar Alhamis 17 ga wata.
Nesirky ya ce, yayin ziyarar wadda za su kammala a ranar Asabar, mambobin tawagar za su tattauna hanyoyin da za a kara samar da taimakon jin kai a kasar.
Bugu da kari, ana sa ran tawagar za ta yi tattaki zuwa garuruwan Bossangoa da Kaga Bandoro ranar Jumma'a don ganin yadda rikicin shafi ayyukan jin kai da kuma ayyukan da ake gudanarwa.
A farkon wannan watan ne jami'an MDD suka bayyana damuwarsu matuka game da tabarbarewar yanayin tsaro a kasar, kana suka yi kira ga gwamnatin wucin gadin kasar, da ta dauki matakan gaggawa don kare rayukan fararen hula daga fadawa cikin hadari tare da maido da doka da oda a kasar.
Kasar ta jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ta shafe tsawon shekaru tana fama da fadace-fadace da rashin kwanciyar hankali, ta kuma sake fuskantar wani rikici a watan Disamban da ya gabata, lokacin da 'yan tawayen Seleka suka kadamar da wasu jerin hare-hare, matakin da ya kai ga sanya hannu kan wata yarjejeniya a watan Janairu, amma 'yan tawayen suka sake kwace Bangui, babban birnin kasar a watan Maris, abin da ya tilastawa shugaba Francois Bozize barin kasar.
Ko da ya ke yanzu an kafa gwamnatin wucin gadi karkashin firaminista Nicolas Tiangaye, wanda aka dora masa alhakin dawo da doka da oda a kasar tare da shirya zabe, amma har yanzu ana ta kara samun fadace-fadace a arewa maso gabashin kasar tun kusan a farkon watan Agusta, lamarin da ya cusa kasar cikin matukar tabarbarewar harkokin jin kai da ya shafi mutane kimanin miliyan 4.6. (Ibrahim)